Ministan ilimi a Najeriya Tahir Mamman ya ce gwamnatin ƙasar ba ta da shirin cefanar da jami’o’in ƙasar ga masu zuba hannun jari.

Ministan ya bayyana haka ne yau yayin wani taro da masu ruwa da tsaki na ma’aikatar.
Malaman jami’o’i a ƙasar ne su ka zargi gwamnatin tarayya da shirin siyar da jami’o’in gwamnati ga ƴan kasuwa.

Sai dai ministan ya musanta batun wanda ya ce gwamnatin ba ta da wannan shirin

A cewarsa, tsarin da gwamnatin ta yi na bayar da dama ga ga mutanen ketare don zuwa su zuba hannun jari a kasar zai taimakawa bangaren ilimi a kasar.
Tahir Mamman y ace tsarin da gwamnatin ta bijiro da shi a buɗe ta yi shi tare da sanar da masu ruwa da tsaki.
Sannan ya bai wa masu ruwa da tsaki dama domin duba tsarin da gwamnatin ta yi na baiwa ƴan kasashen ketare dama don zuba hannun jari a jami’o’in ƙasar.