Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya sun lashi takobin karbe dukkan ikon kujerun shugabanci daga jamiyyun hamayya.

Shugaban kungiyar Bala Mohammed gwamna Bauchi shi ne ya bayyana haka yau a Enugu yayin jawabin buɗe taron ƙungiyar.
A cewarsa, tsarin da su ka yi ya sha bamban da da sauran tsarukan da su ke yi a baya.

Taron dai ya mai da hankali don tattauna ayyukan da su ka shafesu

A cewar Bala Muhammad tsarin da za su fito da su yi zai taimaka wajen karbe madafun iko daga jam’iyyun adawa
An gudanar da taron ne a gidan gwamnatin Enugu.
Gwamnonin jam’iyyar PDP na jihohin Delta, Edo, Filato, Taraba, Zamfara, Oyo da Akwa Ibom.
Sauran sun haɗa da Adamawa, Bayelsa, Eungu da Bauchi ne su ka halarta.