Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar da tsarin ba da lamunin karatu a Najeriya.

Tinubu ya kaddamar da haka ne a zaman zauren majalisar zartarwa da ya gudana yau.

A wajen kaddamar da tsarin akwai sakataren gwamnatin tarayya, da shugabannin majalisar dokoki da wasu daga cikin ministocinsa.

Tinubu ya ce tsarin karatun da gwamnatin ta ƙaddamar zai magance rashin aikin yi da talauci a ƙasar.

A na sa ran dalibai miliyan 1.2 ne za su amfana da tsarin a karon farko.

Shugaba Tinubu ya amince da fitar da naira tiriliyan 35 wanda ake sa ran zai amfani dalibai 70,000 da su ka nema.

Leave a Reply

%d bloggers like this: