Gwamnan Jihar Benue Hyacinth Alia ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf domin fara biya ma’aikatan jihar Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamna ya tabbatar da haka ne a yau Juma’a a wata hira da manema labarai a garin Makurɗi babban birnin jihar.
Gwamna Alia ya ce ya zuwa yanzu gwamnatinsa ta toshe dukkan wata kafa da kudin bautul-malin Jihar ke zurarewa ciki.

A cewarsa gwamnatinsa ta mayar da hankali matuka domin ganin komai ya koma kan hanyar da ta dace a jihar.

Har ila yau gwamnan ya ce bayan taɓarɓare al’amura a Kasar na matsin tattalin arziki, a matakan da gwamnatinsa ta dauki ya fara haifar da ɗa mai ido, sakamakon yadda komai ya fara dawowa kamar yadda ya ke.
Alia ya ce kudaden shigar da Jihar ke samu ya karu kuma dole ne su toshe duk wasu hanyoyin da barayi ke samun damar sata, don ganin nawa za su iya tarawa.
Alia ya ce matukar babu ma’aikata to babu gwamnati saboda haka ya kamata gwamnatinsa ta dauki matakin fara biyan ma’aikata Jihar da albashin naira 70,000.