Kungiyar kare hakkin dan adam ta CLO ta yi fatali da naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi da shugaba Tinubu ya sanya hannu kai, daga bisani kuma kungiyar kwadago ta aminci dashi.

Daraktan Kungiyar kwamared Steve Aluko ne ya bayyana hakan, inda ya ce babu wata hujja da za ta sanya kungiyar kwadago ta amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Daraktan ya kara da cewa kungiyar ta yi watsi da kudin ne sakamakon cewa babu wani amfanin kwarai da kudin za su yiwa ma’aikata a wannan lokaci duba da halin matsin rayuwa da ake ciki.

Steve ya ce a wannan lokacin a kasar babu wani wanda zai yi farin ciki da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Har ila yau ya ce idan aka yi duba da tsadar kayayyaki da kuma matsin tattalin arziki da ake ciki a Kasar ba wanda zai yi murna da karin.
Ya ce a halin yanzu ma’aikatan kasar sun cancanci zama a cikin kyakyakyawar rayuwa ba halin kakaniyaye ba.