Gwamnan Jihar Katsina Umar Dikko Radda ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin aiwatar da hukuncin da Kotun koli ta yanke kan bai’wa kananan hukumomin cin ‘yancin gashin kansu.

Radda ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar a yau Asabar.

Sanarwar ta ce kananan hukumomin Jihar ta Katsina sun dade suna samun wani kaso na cin gashin kansu.

Sanarwar ta ce gwamna Radda ya bayyana hakan ne a gurin wani taron masu ruwa da tsaki da a gudanar a Jihar ta Katsina.

Acewar Radda Jiharsa ta Katsina jiha ce mai bin doka da oda kuma za ta yi aiki ne karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Radda ya bayyana hakan ne bayan Kotun Kolin Kasar ta bai’wa ƙananan hukumomin Kasar cin ‘ ‘yancin gashin kansu biyo bayan wata kara da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin Jihohin Kasar.

Bayan kuma yanke hukuncin majalisar dattawa ta gabatar da kudirin kafa hukumar da za ta dunga gudanar da zaben kananan hukumomin.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: