Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara a Jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’an sun kuma samu nasarar hallaka daya daga cikin wadanda ake zargi, tare kuma da kwato naira miliyan 26.5 a wani sumame da suka gudanar.
Jami’an hukumar reshen Kano ne suka samu nasarar bayan samun wasu bayanan sirri da suka yi akan ‘yan ta’addan, tare kuma da nufar gurin da maharan suke su biyar a wani daji da ke garin Makarfi da ke Kano.

Jami’an na DSS sun isa gurin ne a lokacin da masu garkuwar ke tsaka da rabon kudin fansar da suka ka karba.

Daya daga cikin wadanda jami’an suka kama mai suna Hamisu Tukur ta kama shi ne dauke da raunukan harbin bindiga a tare da shi, ya yin da kuma daya mai suna Bature ya rasa ransa.
Idan baku manta ba dai a makwanni da suka gabata ne dai maharan suka yi garkuwa da mahaifiyar ta Rarara mai suna Hajiya Hauwa Adamu a gidan ta da ke garin Kahutu a karamar hukumar Danja a Jihar Katsina.
Sai dai kuma bayan shafe kwanki 20 a hannun maharan ta kubuta daga garesu.