Hadimin shugaba Tinubu kan yada labarai Bayo Onanuga ya soki magoya bayan dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar Labour Party Peter Obi akan shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar da ake yi a fadin Kasar.

Onanuga ya ce magoya bayan Peter Obi ne ke shirya zanga-zangar da ake yi shirin yi a Kasar a ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.

Hadimin na Tinubu ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a yau Asabar.

A wallafar da Onanuga ya yi ya bayyana cewa magoya bayan Peter Obi ne ke shirin tayar da hargitsi a Kasar.

Hadimin ya kara da cewa ya zama wajibi a ɗora alhaki a kansu akan dukkan abin da ya biyo baya a zanga-zangar.

Onanuga ya bayyana cewa masu shirya zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta Tinubu su ne wadanda suka shiga cikin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020 da ta gabata domin tayar da tarzoma a fadin Najeriya.

A cewarsa masu shirya zanga-zangar su ne mutanen da shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ya ingiza suka gudanar da zanga-zangar barna ta ENDSARS a Najeriya a watan Oktoban 2020 din.

Bayo ya ce bayan zanga zangar ENDSARS ‘yan kungiyar ta IPOB suka shiga jam’iyyar LP a shekarar 2022 domin goyawa Obi baya.

Hadimin na Tinubu ya kuma bukaci ‘yan kasar da su kaucewa yin zanga-zangar duba da cewa magoya bayan Obi ba masu son dimokuradiyya ba ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: