Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane 18 a karamar hukumar Katsina-Ala a Jihar Benue.

Maharan sun hallaka mutanen ne da karfe 11.00 na daren ranar Juma’a a kauyen Mbacher da ke karamar hukumar.

Zuwan ‘yan bindigan ke da wuya suka bude wuta akan mazauna yankin.

Shugaban karamar hukumar Justine Shaku ya bayyana takaicinsa dangane da lamarin, ya ce sai bayan maharan sun gama ta’asarsu jami’an soji suka zo gurin.

Shugaban ya ce maharan sun shiga gida-gida inda suke fito da mutane su na hallaka su.

Shaku ya kara da cewa wasu daga cikin mazauna yankin maharan sun raunatasu a yayin harin.

Sannan ya kuma jajantawa wadanda raunukan ya shafa, tare kuma da jajantawa ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu.

‘Yan bindigar sun ka harin ne bayan gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita daga 6.00am zuwa 6.00pm.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: