Rundunar ‘yan sanadan Babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane Uku da ake zargi da fasa wani gida, inda suka sace zinare da wasu kayayyaki masu kudi a gidan da ke Abuja.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Birnin ACP Olumuwiya Adejobi ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a birnin.
Adejobi ya bayyana cewa an kama mutanen ne bayan wani bincike da kwamitin binciken bayanan sirri IRT ya gudanar, har ta kai ga ya gano wadanda suka aikata laifin.

Ya a yayin binciken, binciken ya nuna babban wanda ake zargi da hannu a lamarin yana sana’ar sayar da kifi ne a kasuwar kifi ta Kado da ke Abuja.

Adejobi ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi wa gidaje uku fashi a unguwar Lugbe da ke birnin.
Ya ce kafin su shiga gida na hudun ne sun yi amfani da wani karfe wajen bankara tagar gidan, inda kuma ta nan ne suka samu damar shiga gidan.
Acewarsu bayan shigar mutanen gidan suka fara bincike domin samun abinda za su sace, inda suka samu damar ganin wata akwati da ke ajiye daga nan ne suka dauka suka tafi da ita.
Kazalika ya ce bayan tafiya da akwatin sun yi amfani da guduma wajen balla murfin akwatin, inda anan ne suka samu kudi, da takardu, kuma zinare a cikin ta.
Har ila yau ya kara da cewa jagoran tafiyar mutanen bayan ganin kayan da ke akwatin ya kira mai saye ya siyar da kayan naira miliyan 60.
Ya ce daga zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci akan abinda suka aikata.