Rundunar yan sanda a Kaduna sun kama wani da ake zargi da satar babura da motoci.

An kama wanda ake zargin da makullai daban daban guda 30 waɗanda za su buɗe babura da motoci.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Manisr Hassan ne ya bayyana haka yau a yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Kaduna

Ya ce wanda aka kama kwararre ne wajen satar ababen hawa na motoci da babura.

Kakakin ya ce a ranar 20 ga watan Yuli da mu ke ciki ne jami’an su ka samu kiran waya inda su ka kama wani Zahradden Suleiman.
An kama wanda ake zargin mai shekaru 35 a duniya a Gulma Road da ke yankin Tsugugi a karamar hukumar Zaria a Kaduna.
Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.