Majalisar wakilai a Najeriya ta shirin soke dokar hukuncin kisa ga mata masu juna biyu.

Kudirin dai ya tsallake karatu na biyu bayan da yar majalisa Fatima Talba ta gabatar da kudirin a zauren majalisar.
Yar majalisar ta gabatar da kudirin ne da nufin sauya hukuncin kisa ga mata masu juna biyu zuwa hukuncin daurin rai da rai.

Yar majalisar wadda ta fito daga jihar Yobe, ta gabatar da kudirin wanda ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar..

Ta ce yanke hukuncin kisa ga mace mai juna biyu ba daidai ba ne domin dan da ke cikinta bai aikata komai ba.
A cewar ta, yanke hukuncin ga mata bai kamata ba mai yiwuwa ne ta haifi yara biyu ko uku ko ma guda daya.
A fatan da take yi, bayan yanke hukuncin daurin rai da rai ta yuwu wani gwamnan ya iya yi musu afuwa.