Dan takarra shugaban kasar Najeriya ƙarƙashin jam’iyar LP Peter Obi ya buƙaci a gaggauta daukar mataki a kan matsatsin da ake ciki a ƙasar.

Obi ya bayyana haka yau Litinin a shafinsa na X.
Ya ce tun da aka fara mulkin demokradiyya daga shekarar 1999 an samu koma baya ga tattalin arzikin musamman a wannan yanayi.

Peter Obi ya buƙaci a samar da daukin gaggawa ga tattalin arzikin Najeriya.

Fadar shugaban kasa dai ta zargi Obi da hannu a kitsa zanga-zangar lumana da ake shirin yi a ƙasar.
Sai dai jam’iyyar Labor Party ta musanta tare da nesanta dan takararta daga hannu a cikin zanga-zangar.
Zanga-zangar lumanar da ake shiryawa dai ta haifar da daga hankalin shugabannin ƙasar Najeriya wanda tun a baya ke ta kiraye-kiraye a janye
Ministan yaɗa labarai a Najeriya ya ce gwamnatin kasar na iya kokarinta wajen kawo karshen matsi da ake fama da shi.