Rundunar yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta buƙaci al’umma birnin da su janye daga shiga zanga-zangar lumana da ake shiryawa a ƙasar.

Kwamishinan yan sandan Abuja Benneth Igweh ne ya bayyana haka yayin holen wasu da ake zargi da aikata fashi da makami a Abuja.

Daga cikin waɗanda aka kama har da waɗanda su ka kashe wani babban tsohon soja a Abuja ranar 22 ga watan Yuni da ya gabata.

Kwamishinan ya ce jami’an na aikin dakile ayyukan ta’adanci a Abuja

Haka kuma ana aikin dakile ayyukansu a jihohin Kaduna Kogi da Nassarawa.

Kwamishinan ya buƙaci a kaucewa shiga zanga-zangar domin rusa zaman lafiyar da ake da shi a Abuja.

Matasa a Najeriya ne ke shirya zanga-zanga bisa halin kunci da matsi da rashin aikin yi da tsaro da ake fama da su a sassan kasar.

Tuni wasu matasa su ke shelanta zanga-zangar lumana ƙasar wadda za a yi tsawon kwanaki goma daga ranar 1 ga watan Agusta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: