Majalisar ɗinkin duniya ta yi gargadi dangane da shirin zanga-zangar da wasu ke shiryawa a Najeriya.

Majalisar ta ce akwai yiwuwar wasu bata gari su yi amfani da damar don cimma bukatarsu

Ɓangaren kula da harkokin tsaro na majalisar dinkin duniya ne ya fitar da bayanan wanda su ka ce sun gano wasu mutane da ke son amfani da damar don cimma burinsu.

Majalisar ta ce a shekarar 2023 an samu fusatattun matasa da su ka fake da fushin chanjin sabon takardun naira a ƙasar su ka far wa wasu bankuna.

Haka kuma shafe kwanaki goma ana zanga-zanga lokaci ne mai tsawo da zai taba tattalin arzikin ƙasa.

Matasa a Najeriya dai na shirya zanga-zangar ne don jan hankalin gwamnati kan tsadar kayan abinci, tsadar man fetur da sufuri da sauran wahalhalu da ake fama da su a ƙasar.

Sai dai gwamnatin ta roki matasan da su janye daga zanga-zangar tare da ƙara mata lokaci don cimma ayyukan da su ka sa a gaba don magance matsalolin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: