Gwamnatin jihar Bauchi ta ce za ta rufe dukkanin da ke karkashin hukumar lafiya matakin farko a jihar yayin zanga-zangar lumana da ake shirin yi a ƙasar.

Wannan mataki ne dai don tsare rayuwar mutanen da ke asibitin da su ka haɗa da marasa lafiya da ma’aikata lafiyar

Shugaban hukumar lafiya matakin farko a jihar Dakta Rilwanu Mohammed ne ya bayyaana haka yayin taron manema labarai a jihar jiya Talata.

Ya ce, rahotannin tsaro sun nuna cewar jami’an lafiya na iya shiga hatsari yayin zanga-zangar a sakamakon haka za su rufe dukkanin asibitoci da cibiyoyin lafiyar.

A yayin zanga-zangar ma’aikatan za su yi hutu don kuacewa fadawa hatsari

Ya ce za su koma bakin aiki ne bayan kammala zanga-zangar.

Ya ce tuni su ka sanar da jami’an tsaro don bai wa hukumomin lafiyar kariya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: