Gwamnatin tarayya ta sake rokon matasan ƙasar da su sake ba ta lokaci, su na masu cewar ba za su sake yin bacci ba har sai komai ya daidaita a ƙasar.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai Mohammed Idris ne ya bayyana haka jim kadan bayan wani zaman gaggawa da aka yi dangane da shirin zanga-zangar lumana da wasu matasa ke shirya wa.

Ya ce sun tattauna a kan batun sannan sun ɗauki matakan da za su kai ƙasar zuwa mataki na nasara.

Aa cewar ministan, dalilin da ya sa ba sa son yin zanga-zangar saboda akwai wasu da ke son fakewa da ita don tarwatsa zaman lafiyar kasar.

A cewarsa, gwamnatin na kokarin ganin ta gana da jagororin zanga-zangar da kungiyoyi don ganin an samar da masalaha.

Sakataren gwamnatin taraya me dai ya kira taron gaggawa a yau wanda aka tattauna dangane da shirin zanga-zangar da matasa ke yi a watan Agusta.

Ministan ya ce al’amarin bai kai ga zanga-zanga ba domin sha’ani ne na cikin gida kuma za a warwareshi.

A cewarsa, sun aan dukkanin matsalolin da su ke damun ƴan ƙasar kuma za su dauki mataki a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: