Wata babbar kotu a jihar Kebbi ta yankewa wani Jamilu Abdullahi hukuncin zaman gidan gyaran hali har sawon rayuwarsa.

Kotun ta samu wanda aka yankewa hukuncin ne da yi wa wata yarinya kurma mai shekaru takwas fyade.
Kotun ta ce wanda aka samu da laifin ya dauki yarinyar ne ya kai ta wani gida da ba a kammala ba a kauyen Dan Warai da ke ƙaramar hukumar Aliero.

Alkaliyar kotun Jusctice Maryam Abubakar ce ta yanke hukuncin bayan gabatarwa da kotun hujuojin da ta gamsu da su.

Ta ce wanda ake zargin ya aikata manyan laifuka bayan gabatar mata da hujjoji da shaidu.
Daga bisani kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon rayuwarsa bayan samunsa da aikata laifin.