Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gana da masu shirya zanga-zangar lumana a kasar.

Majalisar ta ce ta damu da batun tattalin arziki da ake fuskanta kuma zanga-zangar na iya ƙarawa.
Dan majalisa Hon Kingsley Chinda ne ya bayyanawa manema labarai haka a Abuja.

Ya ce majalisar ta buƙaci gwamnatin ta zauna da jagororin zanga-zangar tare da duba bukatun da su ke da su.

Sannan akwai buƙatar tabbatar da cewar gwamnatin ta shiga ciki har a samu masalaha a kai.
Ya ce ba sa goyon bayan zanga-zangar domin a baya wasu bata gari ne ke karbe ragamar tare da juyar da ita zuwa wani abu daban.
Dan majalisar ya ce sun bukaci gwamnatin ta bibiya tare da daukar mataki a kan bangarorin da su ke mafi muhimmanci.
Al’amarin zanga-zanga dai na ci gaba da daukar hankali wanda a yau ma gwamnatin tarayya ta zauna zaman gaggawa don tattauna batun.