Wasu Rahotannin sun bayyana cewa an samu nasarar kwaso wasu gawarwaki 19 daga cikin kogin Ezetu 1 da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa bayan sun yi hadarin jirgin kwale-kwale.

Rahotannin sun bayyana cewa jirgin Kwale-kwalen ya taso ne daga yankin Ekeni inda yana tsaka da tafiya injinsa ya kama da wuta a Unguwar Ezetu 1 da ke gabar Tekun Atlantika da misalin karfe 3 na yammacin ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jirgin ya yi hadarin ne a lokacin da yake kan hanyar zuwa Swali a garin Yenagoa babban birnin jihar a lokacin da injin ya kama da wutar daga bisani kuma ya fashe.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwakin mutane 19 daga cikin waɗanda ke cikin jirgin yayin da masu kamun kifi da jami’an ƴan sandan ruwa ke ci gaba da aikin ceto ragowar.

Bayan gano gawarwakin a daren Jiya Juma’a an kai 16 ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin tarayya da ke Jihar yayin da safiyar yau Asabar aka kai karin wasu uku.
Anashi bangaren Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa da Tattalin Arziki na Jihar Dr Faith Zibs-Godwin tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka karɓi gawarwakin mutanen a ofishin ‘yan sandan ruwa da ke kusa da Asibitin.
Shugaban kungiyar ma’aikatan ruwa na jihar Bayelsa Ipigansi Ogoniba a zantawarsa da manema labarai ya tabbatar da tsamo gawarwakin mutane 19 kawo yanzu.