Gwamnatin Jihar Filato ta sake sanar da sassauta dokar hana fita da ta sanya a Jos Bukuru a Jihar.

Daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na gwamnan jihar Gyang Bere ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Daraktan ya ce sake sassauta dokar zai fara aiki ne daga yau.

Bere ya kara da cewa an sake sassauta dokar ne biyo bayan ingantuwar sha’anin tsaro a yankunan da kuma yadda mutane suka bi dokar.

Kazalika ya ce an sassauta dokar ne bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar.

A don haka gwamnatin Jihar ta bai’wa jama’ar jihar damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Sannan snarwar ta ce gwamnan Jihar Celeb Mutfwang ya mika godiyarsa ga al’ummar Jihar bisa hadin kan da suka bayar a lokacin da aka sanya dokar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: