Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa daga yanzu ba za su lamunci duk wata zanga-zanga da za a gudanar a Jihar ba wadda hukumomin tsaro ba su amince da ita ba.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar.
Sanrwar ta bayyana cewa batagari na amfani da irin wannan damar ta zanga-zangar wajen kwashe kayan gwamnati da na al’ummar Jihar wanda hakan ya sanya ta dauki mataki a kai.

Acewar sanarwar gwamnatin Jihar ba za ta sake lamuntar mummunan zanga-zangar da aka yi a Jihar a ranar 1 ga watan Agsuta da muke ciki ba ya kara faruwa.

Kwamishinan ya kara da cewa barnar da ta faru a ranakun 1 da 5 ga watan Agusta alamu ne bayanannu da ke nuna batagari na shirya yadda za su jefa Jihar ta Kaduna cikin tashin hankali.
A don haka gwamnatin Jihar hadin gwiwa da jami’an tsaro ba za su sanya idanu ba ga masu son ruguza Jihar su cimma burinsu ba tare da daukar mataki akai ba.
Sanarwar ta ce ba za su bar duk wasu batagari ba da ke fakewa da sunan zanga zanga su tayar da tarzoma a Jihar ba.
Aruwan ya ce duk da cewa dokar Kasa ta halartawa mutane yin zanga-zanga, amma haram ne yin duk wani gangami ba tare da amincewar hukumomin tsaro ba.