Jam’iyyar APC ta Kasa reshen Jihar Kano ta yi kira da a gudanar da bincike akan zargin karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai’wa gwamnatin Jihar Kano da wasu jami’an gwamnatin suka yi.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci da a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kwamitin bincike mai zaman kansa.

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan, inda ya nuna damuwarsa akan yadda wasu jami’an gwamnatin jam’iyyar NNPP ke ci gaba da yin sama da fadi da kayan tallafin da ake bai’wa Jihar.

Abdullahi Abbas ya ce rashin daukar matakin da ya dace akai hakan zai sanya zai kasance tamkar goyan baya ga irin wadannan munanan ayyuka na rashin kishin ƙasa.

Shugaban jam’iyyar ya ce ya kawo misalai da dama akan inda aka ga shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai’wa Jihar ciki har da makarantar Sagagi.

Abbas ya kuma zargi gwamnatin ta Kano da canza buhunhunan kayan tallafin da hoton Gwamnan Jihar da tambarin jam’iyyar ta NNPP domin siyarwa ga ƴaƴan jam’iyyar.

Abdullahi Abbas ya sake sokar gwamnatin bisa yadda take bayyana cewa ita ce ta yi ayyukan da gwamnatin tarayya ta yi, irinsu rabon taki da iri ga manoman Jihar.

Da aka tuntuɓi shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Shehu Sagagi ya musanta zargin karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar domin a rabawa mutanen jihar.

Sagagi ya ce shinkafar da aka gani a makarantar islamiyar wacce ya siya ce da kudisa ko wasu suka bayar da sadakarta domin rabawa mutane.

Sagagi ya kara da cewa ya daɗe yana da ɗabi’ar ciyar da yara a makarantar Islamiyyata wanda tun kafin ya zama shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar ya ke yin hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: