Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana damuwarsa akan rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.

Malam Shekarau ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Politics Today’ na gidan talabijin na Channels tv a ranar Juma’a.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa dambarwar masarautar na damunsa amma ba ya son sanya bakinsa a ciki.

A cikin hirar Shekarau ya dora alhakin faruwar rikicin akan ƴan siyasa, inda ya kuma yi fatan cewa za a kawo karshen shi nan ba da jimawa ba.

Malam ya kara da cewa shi babban mamba ne a cikin majalisar masarautar ta Kano, kuma baya ga haka ya yi mulkin jihar, inda ya ce don haka shi babban dan jihar Kano ne.
Kazalika Malam Ibrahim Shekaru ya ce a ranar da maganar masarautar ta je ga kotu, ya ce ba zai sanya baki ba akan rikicin duk kuwa abin da zai faru akan lamarin.
Malam Shekarau ya ce shi dan Kano ne kuma yana son komai na Kano ya kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Acewarsa sunanan suna jira, sannan kuma yana addu’a da a kawo ƙarshen rikicin nan ba da jimawa ba.
Ya ce su na bukatar da a samu kwanciyar hankali saboda suna buƙatar masarautar gargajiya, ya ce ba zai magana sosai akan hakan ba saboda yana daya daga cikin masu rike da saurata.
Ya ce lamarin siyasa ne ya sanya aka tsinci kai a cikin rikicin.
Malam Shekarau ya ce da a ce ƴan siyasa ba su shiga cikin masarautar ba , kuma da an tuntubi masarautun gargajiya ta hanyar da ta dace, da ba a samu wata matsala ba.