Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin babban jojin Nijeriya ta 23 a Kasar.

Shugaban da ya rantsar da ita ne a yau Juma’a a zauren Majalisar tarayya da ke fadarsa a Abuja bayan dawowarsa daga Kasar Faransa.
A halin yanzu Alkaliyar za ta yi aiki ne a matsayin mukaddashiya CJN har zuwa lokacin da Majalisar Dattawa za ta tabbatar da nadin ta.

Shugaba ya rantsar da Kekere-Ekun ne bayan da mai Shari’a Kayode Ariwoola ya yi ritaya a jiya Alhamis bayan cikarsa shekaru 70 a duniya.

Mai shari’a Kudirat ita ce mace ta biyu da ta rike shugabar alkalan Kasar.