Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar lalata gidaje fiye da 200 a Jihar Kaduna.

Shugaban hukumar na Jihar ta Kaduna Dr Usman Hayatu Mazadu ne ya tabbatar da hakan.
Ya ce ambaliyar ta cinye gidajen ne a kananan hukumomin Zaria da kuma Sabon gari duk da ke Jihar a ranar Litinin.
Rahotannin sun bayyana cewa duk da gargadin da hukumomin da abin ya shafa suka yi amma wasu daga cikin mazauna yankin da lamarin ya faru ba su bar guraren ba.

Hayatu ya ce rashin bin umarnin hukumomin da abin ya shafa ne ya haifar da asarar dukiyoyi a yankin.

Shugaban ya ce ya zuwa yanzu gwamnatin Jihar ta Kaduna ta fara daukar matakan kawo karshen matsalolin da ambaliyar ke haifarwa, musamman gyaran magudanan ruwa da kuma wayar da kan jama’a.
Dr Usman ya bukaci mazauna yankunan da aka yi hasashen za su iya fuskantar ambaliyar ruwan da su tashi daga muhallan nasu domin kyaucewa faruwar hakan.
Sannan ya yi kira ga manoma da su yi amfani da filayen da gwamnati ta ba su domin noma, sannan kuma su tashi su koma wasu guraren.