Hukumar zabe ta Jihar Kano ta sauya ranar da za a gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban Hukumar na Jihar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a a Jihar.
Malumfashi ya bayyyana cewa hukumar ta sauya ranar ne sakamakon wasu sauye-sauye da aka samu.

Shugaban ya ce a halin yanzu za a gudanar da zaben ne a ranar 26 ga watan Oktoba, a maimakon 30 ga watan Nuwamba da aka sanya tun da fari.

Kazalika ya bayyana cewa sun yanke shawarar dawo da kwanakin zaben baya ne domin yin biyayya ga Kotun Ƙoli, na bai’wa kananan hukumomin Kasar cin ’yancin gashin kansu.
Acewar Malunfashi jam’iyyun za su fara yakin neman zaɓen ne daga 1 ga watan Satumba sannan kuma su kammala a ranar 25 ga Oktoba.