Wasu mayakan boko-haram hallaka wasu dalibai uku mabiya mazahabar Shi’a a makarantarsu ta Fudiyya da ke karamar hukumar Geidam a Jihar ta Yobe.

Maharan sun kai harin ne a cikin dare, ya yin da daliban ke tsaka da bacci a makarantar ta su da ke unguwar Hausari a Jihar.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa kafin maharan su hallaka daliban sai da suka fito da su waje daga bisani kuma suka bude musu wuta, da misalin karfe 3:44 na daren yau Juma’a.

Wani dan banga a garin na Geidam ya ce, wani dalibi da ya jikkata a yayin harin, a halin yanzu yana kwance a asibiti yana karbar kukawa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar yau Juma’a.

Mataimakin daraktan yada labaran rundunar Operation Lafiya Dole a Jihar Kyaftin Shehu Muhammad ya bayyana cewa zai manema labarai da bayan sun samu karin haske dangane da batun.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: