Kamfanin mai na Kasa NNPCL ya bayyana kudurinsa na mayar da matatun man fetur na Warri da na Kaduna hannun ’yan kasuwa a Kasar.

Kamfanin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma’a.
Kamfanin ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin ci gaba da gudanarwa tare kuma da kula da matatun man biyu da nufin samar da man fetur din da zai wadata a Kasar.

Matatar ta Warri ke Jihar Delta an kafa ta ne a yankin kudu maso kudancin Kasar tun a shekarar 1978.

Matatar na da kuma karfin da za ta iya tace gangar mai 125,000 a kowace rana, tana kuma iya tace wasu sinadaran masu alaka da albarkun man fetur a Kasar.
Sanna kuma an kafa matatar ne da zummar samar da mai ga yankunan kudanci da kudu maso yammcin Kasar.
A gefe guda kuma an kaddamar da matatar mai ta Kaduna da ke Arewacin Najeriya ne tun a shekarar 1980, domin samar da man fetur a yankunan Arewacin Kasar.
Ya yin da Matatar ta ke da karfin tace gangar mai 110,000 a kowace rana.