Akalla mutane 10,291 ne suka rasa muhallansu bisa ambaliyar ruwa da aka samu a karamar hukumar Gummi da ke Jihar Zamfara.

Sarkin Gummi Mai shari’a Hassan Lawal mai ritaya ne ya bayyana hakan, a yayin wata ziyarar gani da ido da gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare ya kai karamar hukumar a jiya Asabar don ganin yadda ambaliyar ta yi.
Mai Shari’a Hassan ya bayyana cewa an samu ambaliyar ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a cikin karamar hukumar, wanda aka shafe kwanaki ana yi.

Sarkin ya ce a yayin ambaliyar ruwan gonaki da dama sun lalace, tare da kadarorin al’ummar Jihar.

A yayin ziyarar jaje da gwamnan ya kai garin ya bayar da tallafin buhunhuna 10,000 na kayan abinci, da barguna, gidan sauro, da kuma tallafin naira 100,000 ga mutanen.
Gwamna Dauda ya kuma shaidawa al’ummar karamar hukumar cewa ,zai tabbatar da ganin an magance matsalar ambaliyar ruwan ta hanyar gina sababbin magudanan ruwa, da gyaran madatsun ruwa da kuma gina sababbin madatsun ruwa domin kaucewa kara afkuwar hakan anan gaba.