Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya nada Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi, bayan mutuwar mahaifinsa Alhaji Yunusa Danyaya a makon da ya gabata.

Mai bai’wa gwamnan Jihar Shawara na musamman kan yada labarai Comred Mukhtar Muhammad Gidado ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce Alhaji Haruna babban dan sarkin, kuma shine zai kasance sabon sarki na 17 mai daraja ta daya.

Sanarwar ta kara da cewa an nada Haruna Danyaya ne, bisa shawarwarin masu nadin sarki, tare kuma da amgani da sashe na 24, da sashi na 3 (1) na dokar Jihar ta Bauchi kan nadin sarakunan gargajiya da kuma sauke su ta shekarar 1991.

Sannan Mukhtar ta ce an kuma mika nadin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Jihar Barista Ibrahim Muhammad Kashim.

Bayan nadinb gwamnatin Jihar Bala Muhammad ya bayyana cewa yana fata Alhaji Haruna zai ci gaba daga inda mahaifinsa ya tsaya, na hada kan al’umma, tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaban masarautar ta Ningi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin Jihar ta Bauchi ta kuma kuduri aniyar tallafawa masarautun gargaji a Jihar, bisa gudummawarsu wajen ci gaban al’umma da samar da zaman lafiya.

Daga karshe gwamna Bala ya yi addu’ar samun gafara da rahma ga mahaifin sarkin Alhaji Yunusa Danyaya bisa rasuwar da ya yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: