Gwamnan Jihar Ebonyi ya tabbatar da kudurin fara biyan ma’aikatan Jihar 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Asabar a gurin babban bikin bude doya na Ojiji Izhi a Jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa tuni ya bai’wa ma’aikatun da abin ya shafa da su samar da hanyoyin fara biyan ma’aikatan Jihar sabon mafi karancin albashin.

Gwamnan na Ebonyi ya ce za a fara biyan ma’aikatan naira 70,000 ne daga watan nan na Satumba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: