Gwamnatin tarayya ta kaddamar da fara ginin gidaje 500 a Jihar Kano.

Ma’aikatar gidaje da raya birane ta tarayya ce ta fara gudanar da ginin gidajen a Jihar ta Kano.
Ginin gidajen wanda aka yiwa laƙabi da “Renewed Hope Estate” ana gudanar dashi ne a Kauyen Lambu da ke cikin karamar hukumar Tofa a Jihar.

Ma’aikatar ta ce aikin ginin gidajen ya hada da gina gida mai dakuna biyu, da mai daki daya, da kuma mai da dakuna uku.

A yayin ziyarar da ya kai don duba yadda aikin ke tafiya, Ministan Ma’aikatar Ahmad Musa Dangiwa ya tununa takaicinsa bisa yadda dan kwangilar da aka bai’wa aikin ya ke tafiyar da aikin nasa.
Dangiwa ya bayyana cewa aikin ginin gidajen ba ya tafiya yadda ya kamata, inda ya bukaci dan gwangilar da aka bai’wa aikin, da ya gaggauta kammala wa ko kuma, gwamnatin tarayya ta kwace daga hannunsa.
Ministan ya kuma bai’wa dan kwangilar mako guda da ya hanzarta kammala aikin ko kuma akwace shi.
Dangiwa ya bayyana cewa su na bukatar ganin an kammala aikin kafin karshen shekarar nan da muke ciki.
Manajan aikin Haruna Lawal ya bai’wa Ministan tabbacin cewa za su karasa kammala aikin kafin lokacin da Ministan ya ba su.