A yau ne shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa kasar China domin fara ziyarar aiki a Kasar.

Hadimin shugaban kan yada labarai Bada Olusegun ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a yayin ziyarar ta shugaban China zai halarci taron Afirka da China karo na tara da za a gudanar a Kasar ta China.

Hadimin Tinubu ya kuma kara da cewa bayan kammala taron shugaban zai kuma gana da shugabannin bangarorin kasuwanci na Kasar ta China.

Ziyarar shugaba Tinubu Kasar ta China ana kyautata zaton za ta kara habaka dangantakar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu da kuma masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.