Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu mutane Goma a gidan a jiya da gyaran hali akan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Kasar.

Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin tsare mutanen a yau Litinin, a zaman da kotun ta gudanar.
Daga cikin mutanen da aka aike da su gidan gyaran halin sun kasance maza Tara, da kuma Mace daya.

Bayan yanke hukuncin kotun ta kuma sanya ranar 11 ga watan Satumban nan a matsayin ranar ci gaba da shari’ar, don duba bukatar neman beli da masu zanga-zangar suka yi.
