Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta Najeriya ta bayyana janyewarta daga yajin aikin da ta shiga na tsawon mako daya, bisa sace daya daga cikin ‘yar kungiyar mai suna Dr Ganiyat Poopola.

Kungiyar ta bayyana janyewa daga yajin aikin ne a yau Litinin ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Dr Dele Abdullahi Olaitan da kuma sakatarenta Dr Ondoaka Christopher Obinna suka fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa, inda ta ce mambobin nata sun koma bakin aikin ne da misalin karfe 8-00 na safiyar yau.

Acewar kungiyar nan da makonni uku masu zuwa Kwamitin Zartarwata na NEC, zai sake zama domin ci gaba da tattaunawa akan batun yin garkuwa da ‘yar kungiyar.

Kungiyar ta ce ta janye daga yajin aikin ne bisa yadda suka hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka dage wajen ganin an ceto Dr Poopola.

Kungiyar ta ce ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da Dr Ganiyat ne tun a watan Disamba shekarar 2023 da ta gabata, da ita da mai gidanta da danta da kuma dan uwan mijin nata, a gidan ta da ke Jihar Kaduna.

Kungiyar ta ce sai dai bayan yin garkuwa da su, a watan Maris din shekarar nan ‘yan bindigar sun sako mijinnata da dan uwansa, ya yin da suka rike Dr Ganiyat ita da dan nata.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: