Rundunar ’yan sandan Najeriya ta yi sanya kyuatar naira miliyan 20 ga dukkan wanda ya kawo mata bayanan da za su taimaka mata wajen kama dan kasar Birtaniya da ta ke nema ruwa a jallo mai suna Andrew Wynne tare da wani abokinsa dan Najeriya mai suna Lucky Ehis Obinyan da ake zarginsu da yukurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata Sanarwa da mai magana da yawun ta Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Litinin.
Rundunar ta bayyana cewa tana neman mutanen ne sakamakon zarginsu da ake yi da cin amanar Kasa, daukar nauyin ta’addan, da kuma hada baki wajen aikita laifuka.

Sanarwar rundunar ta bayyana cewa dukkan wanda ya ga wadanda ake zargin, ya sanar da Ofishin Mataimakin Sufeto-Janar bangaren binciken Kwakwaf da ke Hedikwatar rundunar a Abuja, ko kuma ya kira numbobin da rundunar ta bayar.
