Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayar da tallafin naira biliyan daya da rabi ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.

Allahji Aliko Dangote ya bayar da tallafin ne ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA, domin tallafa mutanen da abin ya shafa.
Sannaan Dangote ya kuma bai’wa gwamnatin Jihar ta Borno tallafin naira miliyan 500, don tallafawa.

Dangote ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar jaje da ya kai Birnin Maiduguri da abin ya shafa, tare da gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule a yau Juma’a.

A yayin ziyarar ta su gwamnan Abdullahi Sule shima ya bayar da tallafin kayayyakin da za a tallafawa al’umomin da abin ya shafa.
A yayin mika tallafin gwamna Babagana Zulum na Jihar ta Borno, ya mika godiyar garesu bisa tallafin da suka bai’wa mutanen da abin ya shafa domin rage musu radadin halin da suke ciki.