Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sake gyarawa tare da inganta madatsar ruwa ta Alau a Jihar Borno.

Ministan ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na Kasa ne ya tabbaatar da aniyar gwamnatin a yayin ziyarar gani da ido da ya kai garin na Maiduguri don ganin barnar da ambaliyar ta yi.
Ministan ya ce za a yi gyaran madatsar ne domin sake kaucewa afkuwar Ambaliyar da aka samu a Jihar a gaba.

Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu tuni an aike da kwararru a fannin domin duuba yadda madatsar ke ciki.

Ya ce bayan kammala duba matsalar za a fara gyaranta cikin gaggawa tare da inganta ta domin sake kaucewa faruwar hakan a gaba.
Ministan ya ce za a tabbatar da ganin ‘yan kwangilar da aka bai wa aikin sun yi mai kyau, sobada gwamnati ba za a bari ayi mara inganci ba.