Hukumar raya yankin Arewa maso gabas NEDC ta yi rabon kayan tallafi ga mutanen da mbaliyar ruwa ta shafa a garin Maidugurin Jihar Borno.

Daraktan hukumar Muhammad Alkali ne ya tabbatar da bayar da kayan tallafin.

Alkali ya ce daga cikin kayan da hukumar ta su ta bayar sun hada da buhunhunan shinkafa 200,000, kwalayen taliya guda 150,000, jarkokin mai 250,000, da barguna 200,000, tabarmi 200,000, rigunan yara 65,000, da gidajen sauro 20,000 da sauransu kayan tallafi a Jihohin Arewa maso Gabashin Kasar.

Alkali ya kara da cewa sun bayar da kayan tallafin ga gwamnatin jihar ta Borno a dakin ajiyar kayayyakin abinci na hukumar ta da ke garin na Maiduguri.

A karshe ya ce za su yi korarin ganin an gyara dukkan gine-ginan madatsar ruwa na Alau da ambaliyar ta lalata a garin na Maiduguri.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: