Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa an tafka makudi a yayin zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Obaseki ya bayyana cewa ayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Jihar, tamkar an yi kwacen mulki ne, wanda hakan kuma ya sabawa dimukradiyyar Kasar.
Gwamnan ya kara da cewa Dumkradiyya da bai’wa kowanne dan Kasa damar zaben wanda ya ke so shugabnce shi.

Godwin Obaseki ya ce karbe mulki da karfi tare da bai’wa wanda bai cancanta ba, kawo nakasu ne ga Dimkuradiyya.

Gwamnan ya tabbatar da cewa a bayyana ya ke an karya dukkan dokokin zaben da aka gudanar a Jihar, inda yayi kira ga wanda aka yiwa makudi da su tafi kotu domin kwato musu dukkan hakkokinsu da aka danne musu.
Sannan gwamna Obaseki ya bakuci mazauna Jihar da su ci gaba da zaman lafiya, duk da cewa an tafka magudi a cikin zaben da aka gudanar.