Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wani fitaccen ’yan bindiga a Jihar mai suna Kachalla Tukur Sharme ya mutu sakamakon wani rikicin da ya barke tsakaninsa da wasu kungiyoyin ’yan bindiga masu gaba da juna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Samuel Aruwa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Aruwa ya ce dan ta’addan shi ne wanda yayi garkuwa da daliban wata makarantar sakandare 121 a garin Kujama da ke Jihar tun a ranar 5 ga Yulin shekarar 2021 da ta gabata.

Kwamishinan ya kara da cewa dan bindigan da yaransa sun gamu da ajalin nasu ne a Dajin Rijana da ke Jihar bayan barkewar rikicin a karshen makon da jiya.

Kwamishin ya bayyana cewa an hallaka ’yan ta’adda biyu na daya bangaren, a musayar wutar da suka yi da juna.
Aruwan ya ce majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa ’yan bindiga biyar ne samu raunuka a rikicin.

Kwamishinan ya kara da cewa dan ta’adda Sharme da yaransa ne ke kai hare-hare a yankunan Millennium City, Maraban Rido, Kujama, Kajuru, Maro, da kuma kauyukan da ke yankin Kateri, da kuma kananan hukumomin Kagarko, Kachia da kuma Birnin Gwari.

Kazalika ya ce ayyukan dan ta’addan ba iya kadai nan ya ba, ya tsallaka har zuwa jihohin Katsina da Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da Jihar ta Kaduna.

Kwamishinan ya kuma ja kunnen mazauna yankunan Rijana da su guji taimakawa dukkan wanda suka gani dauke da harbin bindiga, inda ya bukace su da su kai’wa jami’an tsaro mafi kusa da su bayanan dukkan wanda suka gani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: