Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Kwamishinan zaben a Jihar Farfesa Faruk Adama Kuta ne ya tabbatar da hakan a jiya Lahadi.
Ya ce dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 291,667, inda kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 247,244.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar LP kuwa ya samu ya kuri’u 22,763.
