Jam’iyyar PDP ta Kasa ta yi fatali da sakamakon zaben gwamnan Jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, bayan da hukumar zabe ta Kasa INEC ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmad Umar Fintiri wanda ya kasance shugaban Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ta PDP a Jihar ta Edo ne yayi watsi da sakamakon da hukumar ta ayyana.

Fintiri ya bayyana cewa a yayin sakamakon zaben hukumar ta INEC ta karya dokokin Zaben.

Sai dai a cikin wata sanarwa da sakataren yada lanbaran jam’iyyar na Kasa Debo Ologunagba ya fitar, ya bayyana cewa gwamna Fintiri ya bayyana sakamakon zaben bayan tattarashi ya tabbatar da dan takarar gwamna na Jam’iyyar ta PDP ne ya lashe zaben.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan hakan ne kuma jam’iyyar APC tare da wasu marasa kishi a cikin jam’an INEC suka tafka magudi a cikin zaben.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: