Hukumar kula da yanayi ta Kasa NiMET ta ce wasu daga cikin Jihohin Najeriya za su fuskanci ruwan sama mai karfi a cikin Jihohin.

Hukumar ta kuma ce akwai wasu daga cikin Jihohin Kasar akwai wadanda ruwan ba zai yi karfi sosai ba, inda za a iya kwashe kwanaki uku ana samun ruwan a jere.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa za a yi ruwan ne a akalla Jihohi 17 na Arewa Kasar.

Hukumar ta ce za a fara samun ruwan ne daga yau Litinin, har zuwa ranar Laraba 25 ga Satumbar shekarar nan.

Sanarwar ta ce daga cikin Jihohin da abin ya shafa za a samu ruwan ne mai karfi hade da tsawa a Abuja da kuma Jihohin Neja, Nasarawa, Benue, Filato da kuma Kwara.

Hukumar ta ce za a fuskanci ruwan ne tun daga rana har yammaci, a wasu sassan birnin tarayya Abuja, Neja, Kwara,Kogi , da Benue.

Sanarwar ta bayyana cewa za a iya samun ruwan sama a yau Litinin a Jihohin Sokoto, Kebbi, da kuma Borno.

Yayin da kuma a yammacin yau din hukumar ta ce za a samu ruwan a Jihohin Kano, Jigawa, Borno, Yobe, Taraba, Adamawa, Gombe, Bauchi, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto da kuma Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: