Jam’iyyar PDP ta Kasa ta bayyana cewa ba ta amince da sakamakon zaben gwamnan Jihar Edo da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta sanar ranar Lahadi.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar na Kasa Umar Damagum ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar yau a Abuja.
Jam’iyyar ta ce ko kadan ba ta aminta da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba, bayan kammala tattara kuri’un a zabem da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban ya ce dukkan nin al’ummar Jihar ta Edo sun fito sun zabi dan takarar jam’iyyar ta PDP wanda suke muradin kasancewar ya zamo wanda zai jagorance su.

Damagum yayi kira ga hukumar zaben ta INEC da ta yi amfani da dukkan sauran lokacin da ya rage mata bisa tanadin dokar zaɓe wajen gyara kura-kuran da ta tafka a yayin zaben.
Shugaban ya kara da cewa sai da jam’iyyarsu ta yi zargin jam’iyyar APC da haɗa kai da hukumar ta INEC da kuma mataimakin sufetan ƴan sanda domin kwace mulkin Jihar ta Edo da karfi.