Wasu ‘yan ta’adda a Jihar Yobe sun sanya Bam a cikin layin wutar lantarki wanda ya taso daga garin Damature babban birnin Jihar zuwa garin Maidugurin Jihar Borno.

Kamfanin wutar lantarki na Kasa TCN ne ya tabbatar da aika-aikatar da ‘yan ta’addan suka yi.
Kamfanin ya ce maharan sun yi barnar ne a ranar Asabar din da ta gabata.

Rahotannin sun bayyana cewa layin wutar ya taso ne daga Jihar Gombe, Maiduguri, har zuwa Damaturu a Jihar Yobe.

Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa sanyawa gurin wuta shine karo na uku a cikin watannin da suka gabata, da ‘yan ta’addan ke sanyawa gurin wuta.
Jami’in hulda da jama’a na Kamfanin Ndidi Mbah ya bayyana cewa bayan sanya wutar maharan sun kuma yanke dukkan kafafun da ke rike da layin da ke bayar da wutar.
Mbah ya ce za a bai’wa mazauna garin Damaturu wuta daga tashar wuta ta Pataskum, sannan za a bai’wa mazauna Maiduguri daga tashar wuta da ke cikin birnin.
Bayan kashewar layin wutar hakan ya haifarwa da mazauna garin na Damaturu dana Maiduguri fadawa cikin duhu sakamakon rashin wutar.