Rundunar ‘yan sanda Jihar Borno ta tabbatar da mutuwar kimanin mutane hudu bisa kifewar jirgin kwalekwale da aka samu a cikin Karamar Hukumar Dikwa ta Jihar.

Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Nahum Daso ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Kakakin ya ce lamarin ya faru ne a jiya Litini a yankin Bakassi da ke tsakanin garin Mafa da Dikwa akan hanyar zuwa Maiduguri babban birnin Jihar.

Daso ya bayyana cewa dukkan wanda lamarin ya shafa ’yan unguwar Bulabulin a cikin karamar hukumar, inda aka samu nasarar dauko gawarwakinsu tare da kai su babban asibitin garin Dikwa, daga bisa likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Ya ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu harda mata.

Kakakin ya ce bayan tabbatar da mutuwarsu an mika gawarwaki nasu ga iyalansu domin yi musu sutura.

Rundunar ta kuma jajantawa ‘yan uwan wadnda lamarin ya faru da su, tare da jan kunnen mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa da su kula matuka a wannan yanayi da ake ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: