Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wani mutum dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 19.4 wadda kudin ta ya kai naira biliyan hudu da miliyan 606.

NDLEA ta ce ta kama mutumin mai shekaru 48 a duniya a yau Tatala bayan dawowarsa daga Kasar Ethiopia, inda ya sauka a filin sauka da tashin Jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.

Hukumar ta ce mutumin wanda ya kasance dan Najeriya ne a baya kuma an taba aikewa dashi gidan ajiya da gyaran hali, bisa zarginsa da yin safarar miyagun kwaya.

Bayan kuma aikewa da kotu ta yi dashi gidan gyaran hali ne ya biya tarar da aka yi masa inda aka sake shi, inda ya ci gaba da yin sana’arsa ta yin safarar miyagun kwayoyin a Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: