Shugaban rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa Bai kamata a ci gaba da biyan tallafin man fetur a Najeriya ba domin mutane ba sa amfana da shi.

Alhaji Aliko ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da gidan talabijin na Bloomberg a ranar Litinin, Dangote ya ce bai kamata a ce har yanzu Najeriya ta na biyan tallafin man fetur ba, sakamakon dukkan kasashen duniya sun daina biyan tallafin man.

A cewarsa tallafin da gwamnati ta ke bayarwa, inda wasu mutane suna kara farashin mai, don haka ba bukatar a bayar da tallafin tunda ‘yan Najeriya basa amfana dashi.

Dongote ya ce farashin man Najeriya ya kai kusan kashi 60 na farashin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya inda aka hada iyaka da su domin haka ba ya dorewa.

Alhaji Aliko Dangote na wannan kalami ne bayan fara aikin tace mai da matatarsa ta yi, tare kuma da fitar dashi, da kuma karin farashin litar man zuwa Naira 950 a Jihar Legas, sai kuma fiye da Naira 1000 a yankin Arewacin Kasar.

Dongote ya bayyana cewa samar da tataccen man daga matatarsa ​​zai taimaka mataku wajen rage hauhawar Naira, sannan ya tabbatar da mallakar rijiyoyin mai guda biyu da ake sanya ran za a samu a watan gobe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: